Zazzabin dengue ya hallaka mutane a Burkina Faso
October 21, 2023Talla
Ma'aikatar ta ce ana zargin fiye da mutane 50,000 ne suka kamu da cutar yayin da kimanin 214 suka mutu sanadiyar cutar da ake samu daga sauro a wannan shekarar. An dai samu bullar cutar ce a babban birnin kasar Ouagadougou da kuma Bobo Dioulasso. Alkalumma sun yi nuni da cewa, cutar zazzabin dengue na kashe mutane a kalla dubu 20 a duk shekara a duniya.
A wannan watan ne dai Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi cutar ka iya zama babbar barazana ga wasu kasashen nahiyar Afirka.