1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen gwamna a jihar Anambran Najeriya

November 15, 2013

Wannan zaɓe na zaman irin shi na farko a Najeriya saboda shi ne zakarar gwajin dafin ƙarfin babbar jami'yar adawa ta APC a ƙasar kafin babban zaɓe na shekarar 2015

https://p.dw.com/p/1AIaY
Titel: Parlamentswahl 2011 in Kano State, Nigeria Schlagworte: Nigeria Kano Wahl Wahurne INEC Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch Wann wurde das Bild gemacht?: 9.4.2011 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Sarbi, Kano State / Nigeria Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Parlamentswahl am 9.4.2011 im Dorf Sarbi, Kano State. Wahlurne.
Hoto: DW

Ƙasa da 'yan awoyi da fara kaɗa ƙuri'a cikin zaɓen gwamnan jihar Anambra ɗar-ɗar da rashin tabbas na shirin mamaye harkokin zaben dake zaman zakaran gwajin dafin makomar zaɓukan ƙasar na shekara ta 2015

An dai kai ga jibge jami'an tsaron da babu irin su kuma an ce an ɗauki jerin matakan da babu kamar su duk dai da nufin ɗara sa'a a bangare na jami'an tsaro dama hukumar zaben dake shirin gwada sa'ar su ga zaɓen gwamnan jihar Anambra.

Zaɓen kuma da tuni ya ɗauki hankali a matsayin zaɓen da babu kamar sa cikin ƙasar ta Najeriya da sannu a hankali ke kara kusantar zaɓukan tarraya a cikin halin dar-dar da rashin tabbas.

Duk da cewar dai akwai yan takara kusan goma manyan jamiyyun kasar hudu ne dai tauraron su ke alamun haske a zaben da aka tsara gudanarwa ranar asabar da kuma ke zaman zakaran gwajin dafi ga makomar kasar a zabukan kasar na shekara ta 2015.

Zaɓen na zaman zakarar gwajin dafin ƙarfin babbar Jami'yar adawa ta APC

To sai dai kuma babban rikicin na tsakanin 'ya'yan jami'yar adawa ta APC dake neman kwace mulki da kuma yar uwarta ta PDP dake cikin kawancen sirri da APGA dake mulki a jihar da nufin hana cigaba ta yaduwar APC a cikin yankin na kudu maso gabas dake zaman filin dagar jami'yyun biyu yanzu haka.

Nasarar APC dai alal misali na nufin karin karfi a cikin yankin dama kafajijiyoyin ta a koina cikin fagen siyasar kasar ta Najeriya, a yayin kuma da kawancen na APGA da PDP ke fatan tsaida tasirin APC da ta kama jihar Imo ke kuma neman sabuwar jihar kamawa a cikin yankin

Ko bayan nan dai akwai alaƙa babba tsakanin zaben na Anambra da dan uwansa na tarrayar da kasar ta najeriya ke fatan tabbatar da daidaiton sa da nufin kaucewa tashe tashen hankulan da suka mamaye zabukan kasar na baya

Abun kuma da a cewar Garba Umar kari ke zaman kamar da wuya bisa halin da al'amura ke ciki a fudu da gangaren cikin jihar a yanzu haka

Matakan tsaro lokacin zaɓen

To sai dai kuma koma yaya take iya kayawa a jihar dai ya zuwa ranar yau ra'ayi na banbance tsakanin manyan jam'iyyun biyu game da batun na shirye shiryen zaben da suka hada da takaita zurga zurga tunga karfi shida na yammaciyar yau ya zuwa shida na ranar Lahadi in Allah ya kaimu.

Tijjani Musa Tumsah dai na zaman sakataren jamiyyar APC na kasa, da kuma yanzu haka ke garin Akwa fadar gwamnatin jihar ta Anambra da kuma yace basu rarrabe da halin da jami'an tsaron dama hukumar zaben ke ciki a yanzu ba.

To sai dai kuma koma menene na tunani na adawar dai a nata bangaren dai jam'iyyar PDP tace taji ta gani ta kuma gamsu da abun dake kasa na shirin zaben da a cewar Senator Saidu Umar kumo dake bada shawara ta siyasa ga shugaban PDP na kasa babu kamar sa akan idonsu.

Abun jira a gani dai na zaman mafitar A'in cikin yanayin da sannu a hankali ke kara fitowa fili da halin da demokaradiyar kasar ta Najeriya take ciki.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba