Zaɓen Najeriya: Ƙalubale a fannoni da dama
Ranar 28 ga watan Maris, Najeriya, za ta zaɓi shugaban ƙasa, a zaɓen da ake wa kallon zakaran gwajin dafin jam'iyya mai mulki wadda ke mulki tun bayan da iko ya dawo hannun farar hula.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta na da aiki a gaba
Zaɓuɓɓuka hudu hukumar zaɓen Najeriya ta jagoranta tun bayan da mulki ya koma hannun farar hula, PDP na lashewa, amma a wannan zaɓen ne jam’iyya mai mulki ta PDP take fuskantar zazzafar adawa, kuma ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewar jam’iyyar adawar ta APC na da farin jini. Saboda haka rawar da hukumar zaɓe za ta taka a wannan karon na da muhimmancin wajen ganin ta mutunta hakkin al’umma.
Tsaro babban ƙalubale
Mutane aƙalla milliyan ɗaya da rabi ne suka rasa matsugunensu a yayin da ake kiyasin fiye da mutane dubu 13 sun kwanta dama. Rashin tsaron dai ya janyo tsaiko a fannonin rayuwa da dama kuma yana daga cikin batutuwan da masu zaɓe za su yi la’akari da shi wajen jefa ƙuri’arsu, duk da cewar an sami galaba daga baya.
'Yan gudun hijira: Mu ma muna so a dama da mu
Akwai `yan gudun hijira a ciki da wajen Najeriya, da yawansu waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a, doka ta ce za su iya yin zaɓe ne kaɗai idan sun koma jihohinsu na asali a sansanonin da aka yi musu tanadi, amma duk da cewar sun ce wannan zai yi wahala, burinsu shi ne a dama da su wajen tantance wanda zai jagorancesu a shekaru huɗu masu zuwa.
Majalisa: Ginshiki na tsarin dimokraɗiyya
A majalisar dattawa, jam’iyya mai mulki ce ke da rinjaye, amma ´yan adawa ne ke da rinjaye a majalisar wakilai, hatta kakakin majalisar ma ya sauya sheƙa daga jam’iyya mai mulki ta PDP zuwa ta adawa APC. Sai dai majalisun biyu sun taka rawar gani sossai musamman a bara wajen yanke shawarwari da ɗaukan matakai masu mahimmanci wajen daidaita lamuran ƙasar.
Kafofin sada zumunta: Ƙadangaren bakin tulu ga masu son yin maguɗi
Mutane da dama na samun damar bayyana ra’ayoyinsu dangane da wanda suke so da dalilansu, kuma ko su kansu jam’iyyun suna amfani da shi wajen yaɗa manufofinsu da ma na baya-bayan nan inda aka ga suna amfani da shi sossai wajen yin yarfen siyasa. To amma matasa ba su ɓata lokaci wajen turawa da ma yin sharhi kan duk wani abin da ya sosa musu rai musamman idan bai dace ba.
Limaman tabbatar da zaman lafiya
Ƙungiyoyin addini da na fararen hula sun dukufa wajen faɗakar da al’umma dangane da buƙatar a fita a yi zaɓe, da illar magudin zaɓe, da ma mafi mahimmanci, gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali. Misali Malam Nuraini Ashafa da Fasto James Wuye da ke ƙungiyar nan ta samar da maslaha da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya, na ci gaba na kan gaba wajen cimma wannan buri
Jami’an tsaro: Tubali na daƙile tashin hankali
Duk da cewar al’umma na shakkun nagartan aikin jami’an tsaro, ba su cire ran cewar babu wanda zai yi maganin ɓata gari da masu neman tashin hankali lokacin zaɓe kamar jami’an tsaro ba, kuma suna fata mahukuntan ƙasar za su ba su goyon baya da kayan aiki domin tabbatar da kwanciyar hankali lokacin zaɓe.
Zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki
Ƙungiyoyin fararen hula da dama a yawancin jihohin ƙasar sun ƙulla yarjeniyoyin zaman lafiya dan tabbatar da kwanciyar hankali lokacin zaɓe. Sun yi wannan ne saboda kaucewa rikicin bayan zaɓe makamancin waɗanda aka gani a baya, inda mutane suka rasa rayukansu wasu har yanzu suna rayuwa da irin ɓarnar da ta faru a lokacin.