1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Gangamin neman Mugabe ya yi murabus

Gazali Abdou Tasawa
November 18, 2017

Dubunnan 'yan kasar Zimbabuwe sun gudanar da zanga-zangar a wannan Asabar a birnin Harare domin neman Shugaba Robert Mugabe ya sauka daga kan kujerarar mulki. 

https://p.dw.com/p/2nrQM
Simbabwe Proteste in Harare
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

 

Masu zanga-zangar wadanda wasunsu na dauke da hotunan Shugaba Mugabe yana barci wasunsu kuma da kwalaye masu dauke da kalaman batanci kansa sun yi ta bayyana wakoki na kira ga shugaban da ya yi murabus. Wannan matashi na daga cikin masu zanga-zangar a yau a birnin harare:

Ya ce "Ni dan jam'iyya mai mulki ta Zanu-PF ne amma a yau ina mai ra'ayin lokaci ya yi da ya kamata shugaba Mugabe ya sauka daga mulki kuma tun a yau"

Zanga-zangar wacce ta gudana a cikin lumana a gaban sojoji ta zo ne kwanaki kalilan bayan da sojojin kasar suka karbe kasar tare da tsare shugaba Robert Mugabet a gidansa inda yanzu haka suke can suna kokarin ganin ya yi murabus daga kan mukaminsa a cikin laluma. 

Tsaffin sojojin kasar ta Zimbabuwe wadanda suka yi gwagwarmayar samar wa da kasar 'yanci ne dai suka yi kira zuwa ga wannan zanga-zanga domin tilasta wa shugaban ya yi murabus. Sai dai har yanzu Shugaba Mugabe mai shekaru 93 a duniya da kuma ya share shekaru 37 kan gadan mulki na ci gaba da yin kememe.