1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZimbabwe

Zimbabuwe: Taron 'yan adawa kafin zabe

August 21, 2023

Yayin da aski ya zo gaban goshi a babban zaben Zimbabuwe, sama da magoya bayan jam'iyyun adawa 10,000 sun halarci wani gagarumin taron gangami a Harare babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4VQ8o
Zimbabuwe Gangamin 'yan adawa
Gangamin 'yan adawa gabanin babban zabe a kasar ZimbabuweHoto: KB MPOFU/REUTERS

Masu aiko da rahotannin sun ce dubban jama'ar dauke da tutocin gamayyar jam'iyyun adawa masu launin dorowa sun yi wa babban filin kwallon kafa da ke tsakkiyar birnin kawanya inda suka jaddada goyon baya ga jagororinsu kan mafarkinsu na kayar da jam'iyyar Zanu PF wace ke rike da mulki tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1980.

Karin bayani: Zimbabuwe: Zaben farko ba Mugabe

Zaben shugaban kasar na bana wanda zai gudana a ranar Laraba mai zuwa, zai fi zafi ne tsakanin Nelson Chamisa na jam'iyyar CCC babban mai kalubalantar Shugaba mai ci Emerson Mnangagwa da ake kallo a matsayin dan kama karya.

Karin bayani: Zimbabuwe: 'Yan adawa na Zimbabuwe na cikin matsi

Rashin aiki yi da koma bayan tattalin arziki da cin hanci da kuma hadin kan kasa, su ne manyan kalubale da ke jiran duk wanda zai lashe zaben na Zimbabowe mai cike da sarkiya.