An fara sauraron shari'ar zaben kasar Zimbabuwe
August 22, 2018Talla
Jami'an tsaro dai sun kewaye bangarori daban-daban na Harare babban birnin kasar ta Zimbabuwe cikin shirin ko ta kwana, yayin da kotun zaben ta fara sauraron karar da jam'iyyar adawa ta shigar gabanta, bisa zargin aringizon kuri'a a yayin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a watan Yulin da ya gabata.'Yan adawar dai sun bayyana zaben da cewar yana cike da kura-kurai da kuma magudi a wasu mazabun, tare da neman a sake sabon zabe a kasar. Wannan zabe dai shi ne na farko a kasar bayan da aka tilasta wa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe sauka daga kan karagar mulki.