1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Zanga zangar adawa da takunkumi

Binta Aliyu Zurmi
October 25, 2019

A kasar Zimbabuwe, daruruwan magoyon bayan gwamnatin kasar na zanga-zanga a birnin Harare don yin tir da Allah wadai da takunkuman da Amirka da Tarayyar Turai suka kakaba wa kasar.

https://p.dw.com/p/3RwfG
Simbabwe Beerdigung von Robert Mugabe
Hoto: AFP/T. Karumba

Hukumomin Harare sun ce takumkumin na karya tattalin arziki sun janyo wa kasar asarar biliyoyin kudaden shiga. Shugaba Emerson Mnangagwa kamar marigayi tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya dora alhakin halin da kasar ke ciki akan takunkuman da aka kakabawa kasar na kusan shekaru ashirin tun zamanin tsohon shugaba Mugabe, kan zargin take hakkin dan Adam dama kwace gonakin Turawa fararen fata. 

Shugaba  Emerson Mnangagwa ya ayyana wannan Jumma'ar a matsayin ranar hutu domin jama'a su gudanar da zanga-zanga. Ko da a watan Maris din wannan shekarar Amirka ta kara wa'adin takunkumin da shekara guda a kan wasu kayayakin kasar da kuma wasu jami'ai.