1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jack Straw da Mahamud Azahar a Saudiyya

April 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1T
Hoto: AP

Yau ne a Saudi Arabia, a ke fara zaman taro, tsakanin tawagogin Britania da na Saudiyya, a game da harkokin cuɗe ni in cuɗe ka da ya haɗa ƙasashen 2.

Gabanin wannan taro, sakataran harakokin wajen Britania Jack Straw, ya tantana da yarima mai jiran gado, Sultan Ben Abdel Aziz, a game da huldodi tsakanin Britania da Saudiya, kazalika sun yi masanyar ra´ayoyi ,a kan halin da a ke ciki, a yankin gabas ta tsakiya, mussaman kasar Irak, Palestinu, da kuma rikicin makaman nukleyar kasar Iran.

Nan gaba a yau, tawagogin 2 za su buda taron ,wanda zai bitar harakokin cinikayya.

A hannu daya kuma, ministan harakokin wajen Palestinu Mahamud Zahar, na ci gaba, shima, da ziyara a ƙasar ta Saudiyya.

A taron da su ka gudanar watan da ya gabata, a birnin Khartum na ƙasar Sudan, ƙasashe larabawa sun alkawarta tallafa wa hukumar Palestinawa, ta la´akari, da yadda ƙasashen turai da Amurika, su ka tsuke mata bakin aljihu.

A gam,e da haka hukumomin Saudiyya sun bayyana bada taimakon dala million 92 da yan ka ga gwamnatin Palestinu.

A yau Mahmud Azahar zai gana, da sakataran ƙungiyar ƙasashen musulmi na dunia,, OCI a birnin Jeddah.