1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Al-Bashir a Kenya

August 27, 2010

Kenya ta yi watsi da kiran miƙa shugaba Al-Bashir ga kotun duniya da EU ta yi mata

https://p.dw.com/p/OyBw
Shugaba Omar Al-Bashir.Hoto: picture alliance / abaca

Hukumomin Kenya sun sa kafa sun yi fatali da kiraye-kirayen Ƙungiyoyin duniya na miƙa Shugaba Umar Hasan Al-Bashir na Sudan ga kotun hukunta manyan laifukan yaƙi. Hukumomin na Nairobi suka ce ba su da hurumin kama wani shugaba da ke kan karagar mulki. Shi shugaban na Sudan ya ma koma gida ba tare da ƙasar Kenya ta miƙa shi kamar kamar yadda EU ta buƙata ba. Kantomar harkokin waje na Ƙungiyar ´Gamayyar Turai(EU), wato Catherine Ashton, ta nemi gwamnatin Kenya ta mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da ta amince da su wajen miƙa Al-Bashir. Shi dai Umar Hasan Al-Bashir ya amsa gayyatar da Shugaba Mwai Kibaki na Kenya ya yi masa, na halartar bikin ƙaddamar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar. Sakataren yaɗa labara na Shugaba Al-Bashir, ya bayyana cewa shugaban ya isa fadarsa da ke birnin Khartoum da wannan yammaci.

Mwallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita:Halima Balaraba Abbas