Ziyarar Angela Merkel a Indiya
May 30, 2011A yau ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke fara rangadin aiki a ƙasashen Indiya da Singapor. Gababbnin ziyarar ta, Merkel ta shaidar da cewar tun a shekara ta 2000 ne Jamus ta fara wasu hulɗodinta da Indiya, ƙasar da ta samu bunkasar harkokin kasuwanci na kashi 8.5 daga cikin 100, a bara kaɗai. Shugabar gwamnatin ta Jamus wadda ke wannan ziyara da ministoci biyar, ta ce wannan shine karon farko da ɓangarorin biyu zasu yi ganawar keke da keke.
" Muna da manufofi biyu, zamu iya aiki tare domin bayar da taimakon raya ƙasashe, kana za mu iya tallafawa juna. Sa'annan kuma da ɓangaren kasuwanci domin akwai inda dukkannin ƙasashen biyu suka yi suna saboda ƙwarewa, da kuma ɓangaren Ilimi. Domin Idan yara matasa sun ilimantu, Duniya baki ɗaya za ta ci moriyarsu .A yanzu haka Jamus na ɗaukar nauyin horar da matasa kan ayyuka daban-daban, musamman ta ɓangaren kimiyya".
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Halima Balaraba Abbas