Ziyarar fraministan Kenya a Ivory Coast.
January 3, 2011A yau ne wani kwamitin da ƙungiyar ECOWAS/CEDEAO ta kafa wanda ya ƙunshi shugabannin ƙasashe uku ya sauka a ƙasar Ivory Coast inda zai haɗa gwiwa da Fraministan Kenya, Raila Odinga, wato mai shiga tsakanin da ƙungiyar AU ta naɗa, domin tattaunawa da Shugaba Laurent Gbagbo kan buƙatar ƙungiyoyin ya ba da mulki cikin ruwan sanyi ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Alassane Ouattara.
Duk da irin matsin lambar da yake sha daga ƙasashen ƙetare Shugaba Lauren Gbagbo dai ya ƙeƙasa ƙasa ya ƙi miƙa wa abokin adawarsa Alassane Ouattara mulki, mutumin da duniya ta amince da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da ya gudana cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata. Inda yanzu haka rikicin da ake tafkawa tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu ya yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutane 200.
Tun cikin shekarar da ta gabata ƙungiyar ECOWAS/CEDEAO mai mambobin ƙasashe 15 ta tura shugabannin ƙasashe 3 da suka haɗa da Boni Yayi na Benin, Ernest Koroma na Saliyo da kuma Pedro Pirez na tsibirin Cape Verde domin gargaɗi ga shugaba Gbagbo da ya sauka ko kuma in ya ƙi ya fuskanci tsigewa ta ƙarfin soja, lamarin da shi Gbagbo ɗin ya ce baza ta sabu ba. Jim kaɗan kafin tashinsa zuwa birnin Abidjan, mai shiga tsakani a rikicin na Ivory Coast Raila Odinga, ya bayyana fatan samun nasara a ziyarar tasu.
Ya ce:" Dangane da zuwa na Ivory Coast, ƙungiyar Gamayyar Afirka ta AU ce ta naɗa ni a matsayin mai shiga tsakani kan rikicin da ke faruwa yanzu haka a ƙasar, za mu kuma haɗa gwiwa da wakilan ƙungiyar ECOWAS domin gudanar da tattaunawa da dukkanin ɓangarorin da ke da hannu a wannan rikici, daga bisani kuma mu rubuta rahoto domin ganin yadda za mu samar da ci-gaba"
Shugabannin huɗu dai ana sa ran a wannan karon za su samu damar shawo kan shugaba Gbagbo da ya sauya ra'ayinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar. A cewar mai magana da yawun Raila Odinga fraministan na Kenya zai buƙaci shawo kan wannan matsala ta zaɓe cikin ruwan sanyi. Wadannan kalamai dai sun kasance na sassauci kan wadanda shi Odinga ya yi a baya inda yayi kira ga ƙungiyar AU da ta wasa makamanta domin fatattakar Gbagbo da ƙarfin soja.
A nasa ɓangaren ministan yaɗa labarai na Saliyo, Ibrahim Ben Kargo, wanda shugaban ƙasarsa ke ɗaya daga cikin 'yan kwamitin da za su gana da Gbagbo cewa ya yi babu sauyi kan takardar bayan taron da aka fitar a lokacin bukukuwan krisimati, wadda ta buƙaci lallai Gbagbo ya sauka domin girmama buƙatun 'yan kasar, lamarin da Odinga ma ke wa kallon aiwatar da shi ya zama dole.
Ya ce: " Mutanen ƙasar ta Ivory Coast sun fito fili sun bayyana ra'ayoyinsu cikin ƙuri'un da suka kaɗa, saboda haka akwai buƙatar a girmama waɗannan ra'ayoyi"
Ita dai wannan tawwaga ana sa ran z ata gana da Alassane Ouattara, wanda ya ke ta ƙoƙarin gudanar da gwamnatinsa daga wani Hotel da ke birnin na Abidjan ƙarƙashin kulawar dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya(MƊD). Su dai waɗannan zaɓuka da aka gudanar an yi musu zaton buɗe wani sabon shafi ne kan shekaru 8 ɗin da ƙasar ta share tana fama da yaƙin basasa, wanda ya yi sanadiyyar rabewarta gida biyu wato arewa mai yawan al'umar Musulmi da kuma kudanci da mabiya addinin Kirista ke da rinjaye.
To a maimakon ɗinke wannan ɓaraka tsakanin kudanci da arewacin, sai wata kotun tsarin mulki da ke goyon bayan Gbagbo ta sauya sakamakon da hukumar zaɓe ta fitar wanda aka bayyana Ouatara da lashe zaɓen ta kuma ba wa Gbagbo. Tuni dai MƊD ke zargin magoya bayan Gbagbo da kashe-kashen al'umma gami da ɓacewar magoya bayan zaɓaɓɓen shugaba Alassane Ouattara.
Mawallafi. Tukur Garba Arab
Edita: Halima Balaraba Abbas