1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar IAEA a ƙasar Iran

January 15, 2011

Ƙasar Iran ta ɗauki matakan wanke zargin da ake mata na yunƙurin mallakar makaman nukilya, inda ta gayyaci ƙasashen duniya su kai ziyar ganin ƙoƙob.

https://p.dw.com/p/zy1u
Ali Akabar Salehi, Wakilin ƙasar Iran a hukumar IAEAHoto: AP

A karo na farkon tun bayan shekaru masu yawa, ƙasar Iran ta baiwa jami'an hukumar kula da makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa wato IAEA, damar su kai ziyarar a cibiyar makamashin nukiliyar ta da ke yankin Natanz. Wakilai bakwai daga hukumar ta IAEA suka kai ziyar ganewa idonsu tashar nukiliyar ta Iran. Hukumomi a Tehran sun ce yin hakan, na ya nuna cewa Iran bata da wani abun ɓoyewa a shirin ta na makamashin nukiliya, kuma ta gina shi ne domin samar da zaman lafiya. Wakilan bakwai sun fito ne daga ƙasashen Algeriya, Cuba, Egypt, Oman, Syria, Venezuela da kuma ƙungiyar ƙasashen Larabawa. Bisa bayanan da jamai'an dipalmasiyya su ka bayar, sun ce Iran ba ta gayyaci ƙasashen Burtaniya, Faransa da Jamus ba. Ministan harkokin wajen ƙasar, kuma shugaban hukumar makamashin nukiliyar Ali Akbar Salehi ya ce ƙasar za ta yi amfani da wannan damar wajen bayyana wasu nasarorin da cigaban da ta samu a wannan fannnin. Wannan ziyarar dai ta zo ne 'yan kwanaki kaɗan kafin ƙaddamar da zagaye na biyu na tattaunawar makamashin nukiliyar ta Iran.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Usman Shehu Usman