Ziyarar jakadan Amurka a Koriya ta arewa
June 22, 2007Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Chritsopher Hills yace ganawar sa da mahukuntan Koriya ta arewa ta yi armashi a game da ƙokarin farfado da tattaunawar ƙasashe shida domin kawo ƙarshen shirin nukiliyar Pyongyang. Hills shine babban jamiín Amurka da ya ziyarci Koriya ta arewa tun tsawon shekaru biyar da suka wuce. Ziyarar ta zo ne yan kwanaki kaɗan bayan da Koriya ta arewa ta gaiyaci jamián bincike na hukumar makamashin nukiliya ta majalisar ɗinkin duniya zuwa ƙasar, domin fara aiwatar da shirin rufe tashar nulikiyar Yongbyon. A watan Fabrairun da ya gabata, Pyongyang ta yi alƙawarin rufe tashar nukiliyar, a taron kasashe shidda da ya gudana a Beijin, to amma daga bisani taƙi har sai an sakar mata miliyoyin kuɗaɗen ta na ajiya da Amurka ta riƙe a bankin Macau. A makon da ya gabata ne dai Koriya ta arewan ta tabbatar da cewa ƙudaden sun shiga cikin lalitar ta.