Ziyarar Kofi Annan a birnin Teheran
September 4, 2006A ziyarar da ya kai a birnin Teheran, Kofi Annan bai gabatar wa shugabannin ƙasar Jumhuriyar Islama ta Iran wani sabon tayi ba. Ya dai yi kira gare su ne da su koma kan teburin shawarwari, don a ci gaba da nemo hanyoyin sulhunta rikicin da ake yi kan shirye-shiryen da ƙasar ta sanya a gaba, na mallakar cibiyoyin samad da makamashi da fasahar nukiliya.
A cikin jawabinsa a birnin Teheran, Kofi Annan, ya yi kira ga duk ɓangarorin da wannan lamarin ya shafa, da su nuna haƙuri da dauriya wajen sulhunta rikicin ta hannunka mai sanda, tare da ƙarfafa cewa, takunkumi ba shi ne zai warware matsalar ba. Babu shakka wannan jawabin dai ba zai faranta wa fadar White House rai ba. Shugaba Mahmoud Ahmadinijad kuma, bai nuna wata damuwa ga batun sanya wa ƙasarsa takunkumi ba. Bisa dukkan alamu, mahukuntan birnin Teheran ba sa bukatar Majalisar Ɗinkin Duniya ta kasance mai shiga tsakani, wajen nemo hanyoyin sulhunta rikicin. Bayan cikar wa’adin da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya bai wa Iran, yanzu yaƙin cacar baka ake yi tsakanin birnin Teheran da ma’aikatar tsaro ta Amirka.
Har ila yau kuma, a kwamitin sulhun, an gaza cim ma daidaito kan inda za a nufa bayan zartad da ƙuduri mai lamba 1696. Shin haƙuri za a yi da tafiyar hawainiyar da ake yi a shawarwari da Iran ɗin, ko kuwa za a zartad da ƙudurin sanya mata takunkumi ne? Wannan dai ita ce tambayar da ba a samo amsar ta ba tukuna kawo yanzu. Su dai ƙasashe guda biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun da kuma Jamus, ƙoƙarin kare matsayinsu suke yi bayan cikas ɗin da Kofi Annan ya samu a ziyararsa a birnin Teheran.
Game da batun sanya wa Iran ɗin takunkumi dai, ana ta ƙara samun rashin jituwa tsakanin masu adawa da shirin makamashin nukiliyan ƙasar Jumhuriyar Islaman. Yayin da Berlin ke neman a ƙara anagaza wa Iran ɗin a huskar diplomasiyya, birnin Paris na kira ne ga ci gaba da tattaunawar da ake yi, London kuma na neman a yi taka tsantsan. Birnin Beijing kuwa, tana neman a sake tsarin tinkarar batun ne ma gaba ɗaya, yayin da Moscow, ita take barazanar hawar kujerar na ƙi ga duk wani yunƙurin sanya wa Iran ɗin takunkumi. Wato a halin yanzu dai, mahukuntan birnin Washington ne kawai ke neman a aiwatad da ƙa’idojin da ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniyar ke ƙunshe da su, har da ma nasu ƙarin.
A ganin masharhanta da dama dai, wannan rashin jituwar da aka samu tsakanin ƙasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun, zai ƙara ƙarfafa wa Iran gwiwa wajen cim ma burinta. Za a iya ma cewa, a gwagwarmayar da aka yi tsakanin Iran da kwamitin sulhun kawo yanzu, kwamitin ne ya sha kaye.
Yanzu kam babu wani zaɓi, face yin haƙuri da kuma ci gaba da tattaunawa da mahukuntan birnin Teheran, kamar yadda babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya bukaci a yi.