150811 Kenia Niebel
August 15, 2011A lokacin da Dirk Niebel ya isa Nairobi babban birnin ta Kenya ruwa aka yi ta yi kamar da bakin ƙwarya. Amma kuma yayin da ya kama hanya zuwa birnin Mombasa, ba abin da ya gani illa komabaya da rashin ruwan na sama ya jefa wasu sassa na ƙasar a ciki. Daidai da gonakin masara a garin Mindali sun yi bushewar da ba za iya samun damar shuka ba, ballatana ma a yi maganar samun albarkar gona. Lucy Munyeke ta ce ƙamfar ruwan sama da suka fiskanta a shekarun baya, ya jefa su cikin wani mummunan hali na rayuwa.
"Babu inda ake samun ruwa a lokacin fari fashe a cikin ƙududdufi."
Baƙar wahala mazauna garin na Mindali suka yi ta sha kafin su cimma ƙududdufin da suke ɗebo ruwa. Sai dai sun fara samu sa'ida tun bayan da ƙungiyar nan ta Jamus da ke bayar da taimakon jinƙai wato Welthungerhilfe ta kafa tankoki biyu domin samar da ruwa mai tsafta ga mabukata. Ita dai wannan ƙungiya ta yi amfani ne da dabaru na zamani domin tara ruwan sama da aka yi tun watan afrilu, tare da tsaftace shi.
Mutane dubu uku ne suke cin gajiyar wannan shira na Jamus bisa biyan kuɗin da bai taka kara ya karya ba. Da wannan kuɗin ne ma wasu 'yan garin Mindali ke amfani wajen sayen sinadarai da ake bukata domin ci gaba da aimen wannan hanya ta samar da ruwa. A cewar Johan van de Kamp na ƙungiyar Welthungerhilfe, laƙantar da waɗanda abin ya shafa dabarun samar da ruwa mai tsafta ce, hanya mafi a'ala a garesu.
"Wannan wani mataki ne na taimakon kai da kai. Da zarar suka saba ji daɗin amfani da wannan ruwa, za su yi tsayuwar daka domin ganin cewar sun alkinta shirin."
Makamancin wannan shiri na tarar ruwan sama, tare da tace shi, aka yi amfani da shi a Ngnagani domin samar da ruwa mai tsafta a makarantar firamaren na garin, bisa tallafi iyayen yara. A cewar hedmasta na wannan makaranta, wannan shiri ya sa sun shawon kan matsalolin da karancin ruwa ke haddasa musu.
"Wannan tsari ya sa yara na zuwa makaranta . kana lafiyarsu ta inganta domin suna wanke hannu bayan sun je ban ɗaki, ko kuma idan suka ci abincin da ake dafa musu a wannan makatanta. saboda haka babban ci gaba ne a garemu."
Kyautata halin rayuwar mazauna karkarar Kenya da wannan shiri na tara ruwan sama ya yi ne, ya sa ministan tarayyar Jamus da ke kula da al'amuran raya ƙasashe masu tasowa Dirk Niebel, yin kira da a rungume shirin hannu biy-biyu a cikin ƙasashen da ke ama da fari. Kana ya neme su da su rungumi tsari noma da ke jure wa fari, tare da tara ragowar abinci a runbunan ajiya domin fiskantar matsalar abinci a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Niebel ya ce miliyon 700 na euro jamus za ta ware domin agaza ma wannan shiri a duniya, a wani mataki na kandagarki ga matsalar fari.
"Babu wata saddabaru da za a yi domin kauce ma fari kwata kwata. Amma kuma za a iya ɗaukar matakan tinkarar wannan bala'i, tare da dogaro akansu domin samun sa'ida."
'yan Somaliya dubu 400 da rikici da kuma 'yunwa suka koro, da kuma suke tsugune a sansanin Dadaad, na daga cikin waɗanda ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirka Niebel zai je gane halin galabaita da suke ciki a gobe talata.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala