Ziyarar ministan tattalin Jamus a Indiya
April 4, 2005An saurara daga bakin ministan tattalin arzikin na Jamus, jim kadan kafin tashinsa daga Berlin yana mai bayanin cewar akwai bukatar kara fadada huldodin tattalin arziki tsakanin Jamus da Indiya kuma fadar mulki ta New Delhi na yin kira ga ‚yan kasuwar Jamus da su kara yawan jari da suke zubawa a kasar indiya mai samun bunkasa a cikin gaggawa. A halin yanzu haka reshen kamfanin Siemens a New Delhi da Bangalore da Kalkutta na da ma’aikata sama da dubu daya da 300 sakamakon bunkasar da yake samu a harkar sadarwa, inda a yanzu haka kasar ta Indiya take da layukan tarfo kimanin miliyan 90. An kuma kyasce cewar adadin zai ribanya sau uku a cikin shekaru uku masdu zuwa. A lokacin da yake bayani game da haka Werner Schachermeier, darektan reshen kamfanin Siemens a kasar indiya cewa yayi:
Kasar indiya na daya daga cikin kasashen da ba a daukarsu da muhimmanci, amma duk wanda ya nazarce bunkasar da take samu a harkar zuba jari musamman a fannin sadarwa zai yi mamakin wannan ci gaba. Gwamnati na da niyyar zuba abin da ya kai dala miliyan dubu 16 a wannan bangaren a cikin shekaru uku masu zuwa.
Shi dai kamfanin Siemens na da tarihin sama da shekaru 100 a kasar Indiya, kuma a yanzu haka shi ne na biyu wajen sayar mata da kayan gyara na spare. Kamfanonin Jamus na iya taka muhimmiyar rawa a harkar sufuri a cewar ministan kudi na kasar Indiya Chidambaram, kuma bai kamata su yi sake da wannan dama ba. An ware tsawon yini biyu domin tattaunawa tsakaninsa da ministan kudi na Jamus Wolfgang Clemen dake samun rakiyar ‚yan kasuwa 45. Tun da dadewa kamfanonin Amurka da Birtaniya da na sauran kasashen Asiya suka kutsa kai a wannan gagarumar kasuwa dake dada samun bunkasa ba kakkautawa. Dangane da Jamus kuwa, muhimmin abin da ake bukata shi ne kafa kamfanoni na hadin guiwa tsakanin sassan biyu. A shekarar da ta wuce an samu bunkasar kashi 22% a huldar cinikin Jamus da Indiya. Amma a bangaren zuba jari har yau akwai mummunan gibi, in ji Dietrich Kebschull, wanda tun shekaru 20 da suka wuce yake bakin kokarinsa wajen daga matsayin dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Ya ce kasar Indiya dai tamkar wani kyakkyawan dandali ne na zuba jari kuma tana da wadatacciyar kasuwa ta la’akari da yawan al’umarta su sama da miliyan dubu daya.