1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Schröder a Indiya

October 7, 2004

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard schröder da takwaransa P/M Indiya Manmohan Singh sun yi alkawarin daukar nagartattun matakai domin karfafa huldodin cinikayya tsakanin kasashen biyu

https://p.dw.com/p/Bvfr
Schröder a Indiya
Schröder a IndiyaHoto: dpa

A halin da ake ciki yanzu haka akwai kyakkyawar dama ta karfafa huldodin dangantaku tsakanin Jamus da Indiya. Dalilin haka kuwa shi ne kyautatuwar da aka samu ga yanayin hadin kan tattalin arziki tsakaninsu kuma dukkan kasashen biyu na rufa wa juna baya a kokarin neman wata kujera ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD. A zamanin baya dai an sha fama da tafiyar hawainiya a kokarin da kasashen na Jamus da Indiya suka rika yi domin karfafa huldodin ciniki tsakaninsu, musamman ma idan aka yi la’akari da cewar huldar ciniki tsakanin Jamus da China ta ribanya wacce ke akwai tsakanin Jamus da Indiya har sau goma, kamar yadda shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya rika nanatawa a ziyarar tasa ta yini biyu ga fadar mulki ta New Delhi. Wani abin dake taka rawa a game da wannan ci gaba kuwa shi ne kasancewar duk wani dan kasuwar da ya kai ziyara kasar China zai shaidar da bunkasar tattalin arzikin da kasar ke samu ba kakkautawa. Kuma ko da yake yawan bunkasar da Indiya ke samu a shekarun baya-bayan nan bai gaza na kasar China ba, amma babu wata shaidar dake yin nuni da hakan a zahiri. Zuba jari a Indiyan kuwa abu ne da zai samar da kyakkyawar riba ga kamfanonin Jamus fiye da yadda lamarin yake dangane da sauran kasashen Asiya. A ganawar da suka yi, shugaban gwamnatin jamus Gerhard Schröder da takwaransa P/M Indiya Manmohan Singh, sun ci alwashin kara karfafa huldodin cinikinsu domin cimma ribanyen abin dake akwai a yanzun, nan da shekaru biyar masu zuwa. A baya ga maganar tattalin arziki, huldar siyasa na taka muhimmiyar rawa a tsakanin kasashen Jamus da Indiya, saboda kowace daga cikinsu na fafutukar neman dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDD. Kazalika dukkan kasashen biyu na fatan karfafa matsayin MDD da kuma gusar da dukkan tabon da aka gada na rarrabuwa a zamanin yakin cacar baka tsakanin kasashen yammaci da na gabacin duniya. A wancan lokaci Jamus bata da muhimmanci ga kasar Indiya, wacce ta fi mayar da hankalinta ga washington da London da Paris a manufofinta na ketare, Amma a yanzu al’amura sun canza suka dauki wani sabon salo a huldodin dangantaku na kasa da kasa. A sakamakon haka tun a shekara ta 2001 Jamus da Indiya suka cimma daidaituwa akan saduwa tsakanin shuagabannin kasashen, ko da akalla, sau daya ne a shekara, kuma wannan shi ne karo na biyu da Schröder ya kai ziyara fadar mulki ta New Delhi.