Najeriya: Buhari ya ziyarci Maiduguri
February 12, 2020Ana dai ganin ziyara ta Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriyar, na da nasaba da hare-haren da mayakan Boko Haram ke zafafa kai wa a 'yan kwanakin baya-bayan nan a jihar ta Borno, musamman harin da suka kai garin Auno da mutane sama da 30 suka riga mu gidan gaskiya. Shugaba Buhari wanda ya sauka a Maiduguri da misalin karfe 1:05 na ranar Larabar wannan mako kai tsaye daga kasar Habasha bayan kammala taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka AU, ya samu tarba daga gwamnan jihar Borno, inda suka yi ganawar sirri.
Sai dai wakilinmu a Maidugurin Al-Amin Suleiman Muhammad ya ce shugaban bai ziyarci garin Auno domin ya ganewa idanuwansa abin da ya faru ba, duk da fatan hakan daga al'ummar yankin gabanin ziyarar tasa. Koda a Larabar wannan makon ma, rahotanni sun nunar da cewa jami'an tsaro biyar ne ciki har da sojoji biyu suka rasa rayikansu, a wasu jerin hare-haren ta'addanci da aka kai a wasu yankuna na jihar ta Borno, kamar yadda wata majiya ta shaidar.