ƙaddamar da sabon kundin tsarin Kenya
August 27, 2010Shugaba Mwai Kibaki na Kenya ya rattaba hannu akan sabon kundin tsarin mulkin ƙasar domin bayar da damar fara aiki da shi a yau. Daga cikin sauye-sauye da kundin da zaɓen jin ra'ayin jama'a na 4 ga watan Agusta ya bayar da damar yi ma gyaran fiska, har da rage ƙarfin ikon shugaban ƙasa.
Shugabannin Afirka da dama ne suka halarci bikin ƙaddamar da sabon kundin tsarin mulkin a Nairobi, ciki kuwa har da shugaba Umar Hasan Al-Bashir na Sudan da kotun hukunta manyan laifukan yaƙi ke neman gurfanarwar gaban ƙuliya.
'Yan tawayen Darfur da kuma ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Right Watch sun yi kira ga hukumomin kenya da su miƙa Al-Bashir ga kotun da ta amince da kafata. Sai dai hukumomin Kenya sun bayyana cewa ba su da hurumin kama shugaban wata ƙasa da ke kan karagar mulki.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu