1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

230711 Anschläge Norwegen

July 23, 2011

A ƙasar Norway ana ci gaba da tattara bayanai kan musabbabin harin ta'addanci mafi muni a ƙasar tun bayan yaƙin duniya na biyu, inda kusan mutane 100 suka mutu, sakamakon harin bam a birnin Oslo da kuma harbin bindiga

https://p.dw.com/p/122IT
Oficin Frai ministan Norwa da aka kaiwa hariHoto: dapd

Harin ta'addancin da aka kai da bam da kuma harbin wasu matasa da aka yi kimanin 85 da aka yi, ya sa ƙasar Norway ta kaɗu. Kawo yanzu 'yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekaru 32 da ake tuhuma da yin harbin. Kawo yanzu an fara mayar da martani daga ciki da wajen ƙasar ta Norway.....

Ɗaukacin ƙasar Norway dai tana cikin wani makoki, bayan harin bam da aka kai tsakiyar babban birnin ƙasar wato Oslo, da kuma wani harbin da aka yi a tsibirin Utoeya da ke kilo mita 40 daga birnin na Oslo. Jami'an tsaro sun bayyana cewa suna riƙe da wani matashi da suke tuhuma da harbin matsan da aka yi a tsibirin Utoeya. Ɗan shekaru 32, wanda suka ce yana cikin masu tsatsauran ra'ayi na ƙasar ta Norway, kuma kawo yanzu yana taimaka musu a tambayoyin da ake ci gaba da yi masa. kamar yadda wannan jami'in 'yan sanda ke cewa.

Doppelanschlag Norwegen - Anders Behring Breivik
Anders Behring Breivik shine saurayin da ke tsare ana tuhumarsa da harin a tsibirin UtoeyaHoto: picture alliance/dpa

"Mun kama wani mutum, amma hakan ba wai yana nufin babu ƙarin wasu da ke da hannu ba. Sai dai a nan gaba abinda muka gano, za mu bayyana wa duniya komai"

an yi harbin ne a tsbirin Utoeya

Ita kuwa wannan yarin'yar tana daga cikin matasan da aka kaiwa harin.

Flash-Galerie Doppelanschlag Norwegen
Matasan da aka kaiwa harinHoto: dapd

"Haka kwatsam sai muka fara jin harbi, wasun mu sukace wani ne yake mana wasa, sai muka ga abokanmu na gudu, mu kamar ashirin sai muka raɓe cikin bishiyoyi, sai na yi tajin kowa na cewa wayyo Allah, daga nan sai muka rude, nan take sai na ga wasu abokanmu kwance a ƙasa jina-jina, ɗaukacin inda muke zaune, ya cika da jini"

Wannan harin da aka kai a ƙasar ta Norway ya zo bazata, domin ƙasa ce da ba'a cika samun tashin hankali ba. Don haka Firai ministan ƙasar Jens Stoltenberg yace...

"Abun yana da ciwo ta ko'ina, wannan tsibirin da aka kai harin, wuri ne da nake zuwa shaƙatawa tun sheakru 37 da suka gabata. amma wannan tsibirin ya samu kansa cikin tashin hankali. A ƙasa da sa'a guda ya kasance wani wurin bala'i"

Martanin ƙasashen duniya

Nan take dai ƙasashen duniya kuwa suka fara yin Allah wadai bisa wannan harin ta'addanci. Shugaban ƙasar Amirka Obama cewa ya yi.

Obama Nobelpreisverleihung
Obama da matarsa Michelle a tare da 'Yangidan sautar Norway a Fadarsu dake OsloHoto: AP

"Ina tunawa da irin kekkewar tarba da 'yan ƙasar Norway suka yi min a ziyar da na kai Oslo. Don haka ɗaukacin zukatammu na tare da su. Kana za mu bada dukkan goyon bayan da za mu iya bayarwa, a dai-dai lokacin da ake ci gaba da binciken wannan ta'asar"

Kazalika ƙasar Jamus da take maida martani kan harin, ministan harkokin wajenta Guido Westerwelle, ya bayyana yadda suka ji da harin da laƙume rauyuka.

"Mun kwatanta wannan mummunan harin a matsayin wani raɗaɗi ga 'yan ƙasar Norway. Ba a son dalilin kai shi ba, amma abin da ke a zahiri shine, babu wata hujja ta kai wannan harin rashin imani"

Explosion in Oslo
Sojoji da msu aikin ceto a tsakiyar birnin Oslo,Hoto: dapd

Tunani dai ya fara sauyawa, inda da fari a ka ɗauki cewa harin wasu 'yan ta'addane daga waje, sai dai yanzu hankali ya karkata ga masu tsattsauran ra'ayi na cikin gida. Domin 'yan sanda a ƙasar ta Norway sun bayyana cewa sun fara samun wasu ƙarin haske, a saurayin dake cikin ƙungiyar kiristoci masu tsatsauran ra'ayi na ƙasar wanda suka cafke. Sai dai kawai bincikene zai nuna gaskiya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala