1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Saudiyya ta nuna goyon baya ga yunƙurin da gwamnatin Iraqi ke yi na samad da zaman lafiya a ƙasar.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burw

A farkon ziyarar da yake kai wa ƙasashen yankin Gulf, Firamiyan ƙasar Iraqi, Nuri al-Maliki, ya ya da zango a Saudiyya, inda mahukuntan ƙasar suka tabbatar masa da cikakken goyon baya a yunƙurin da yake yi na kawo ƙarshen zub da jini a ƙasar. A wata ganawar da ya yi da Firamiyan jiya daddare, yarima mai jiran gado na Saudiyya, Sultan bin Abdul Aziz, ya kyautata zaton cewa sabuwar gwamnatin Iraqin za ta iya tabbatad da zaman lafiya da tsaro a ƙasar, sa’annan kuma ta kawo ƙarshen wahalhalu da matsin halin rayuwa da al’umman Iraqi ke huskanta a halin yanzu.

A cikin Iraqin da kanta dai, shirin da Firamiya al-Maliki ya gabatar na huskantar adawa daga shugabanin ’yan ɗariƙar Sunni da kuma ƙungiyoyin ’yan tawaye.