250809 Kenia Volkszählung
August 25, 2009Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10 da wannan ƙasa dake gabashin Afirka ke ƙidayar jama´arta. Taƙaddamar da ake dai shi ne tambaya game da ƙabilun mutane. Masu sukar lamiri na fargabar cewa ana iya amfani da bayanan a hanyoyin da ba su dace ba. To sai dai gwamnati ta ce tara waɗannan bayanan yana da muhimmanci musamman bisa la´akari da mummunan rikicin ƙabilancin da ya auku a ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasa kimanin shekaru biyu da suka wuce.
Shugaba Mwai Kibaki a lokacin da yake magana ta gidan telebijin ɗin ƙasar ta Kenya ya ce lokaci yayi da za a yi ƙidayar mu baki ɗaya.
A karon farko cikin shekaru 10 gwamnatin Kenya ta fara tattara bayanai game da yawan al´umar ƙasarta. Sama da jami´ai 140.000 ne suke tafiyar da wannan aiki inda zasu shafe tsawon mako guda suna bi gida-gida don yiwa mutane tambayoyi. To sai dai ba duka ´yan ƙasar ne suka sha´awar ba da amsoshin tambayoyin ba, musamman game da ƙabilar mutum. Domin hakan na yi musu tuni da mummunan arangamar da aka yi bara biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda wani mai gadi da ake kira Dennis mai shekaru 29 ya nunar.
"Bana jin yana da kyau su yi tambaya game da ƙabilarka musaman saboda rikicin bayan zaɓen shugaban ƙasa. Muna ganin wannan mataki ka iya san tsoro a zukatan mutane cewa wannan rikicin ka iya sake faruwa."
Yayin wannan rikici ƙabilun ƙasar ta Kenya sun shafe makonni suna kaiwa juna hare-hare wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1400 sannan wasu dubu 600 suka tsere daga gidajensu kuma har yanzu da yawa daga cikinsu ba su koma ƙauyukansu ba.
Yanzu haka dai wata ƙungiya ta yi kira da ka da a amsa wannan tambaya game da ƙabilar mutum. Shugabanta Reginald Okumu ya ce ana iya amfani da wannan bayani a hanyoyin da ba su dace ba.
"Shin za a yi amfani da wannan ƙididdigar ne don gina makarantu na musamman ga wasu ƙabilu ko gina musu hanyoyin mota? Tun bayan samun ´yancin kai, tun shekaru 46 da suka wuce an yi ta auratayya tsakanin ƙabilu daban daban na Kenya yayin da wasu suka saje da wasu. Ta haka an samu wani sabon yanayi. Wasu ma ba su iya harshensu na asali ba."
Okumu yayi tuni da ƙasar Rwanda inda gabanin kisan ƙare dangi da ya auku, an tara bayanai game da ƙabilun ƙasar. Bai kamata Kenya ta tabƙa irin wannan kuskure ba musamman bisa la´akari da abin ya faru a bara.
To sai dai hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta ce ba ta ga wata alaƙa a nan ba. Daraktanta Collins Opiyo na da ra´ayin cewa duk wata ƙidayar jama´a da za a yi ba tare da an san ƙabilarsu ba to babu ƙwarewa a cikin aikin.
"Wannan tambaya tana da muhimmanci na al´adu. Zata ba da damar sanin ɗabi´unsu da yadda suke rayuwa da alƙalumma na yawan haihuwa da mace-mace. Sanin koma ne cewa halayar wasu ƙabilun na da mummunar barazana ga lafiyarsu."
Nan da watanni uku hukumar za ta fara ba da sakamakon na ƙidayar jama´ar sannan a ba da cikkaken bayani a cikin shekaru biyu masu zuwa.
Mawallafa: Antje Diekhans/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi