Ƙoƙarin warware rikicin Nukiliyar Koriya Ta Arewa
December 22, 2007Talla
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta buƙaci Koriya ta arewa kawo ƙarshen ayyukan cibiyoyinta na Nukiliya. Yin hakan a cewar Rice, abune da zai tabbatar da cika alƙawarin data ɗauka a tattaunawar sulhu ta ƙasashe shiddan nan. Koriya ta arewa dai tayi alƙawarin halaka cibiyar makaminta na Nukiliya dake Yongbyon, a hannu ɗaya kuma da bayar da cikakken bayanin shirin Nukiliyarta a ƙarshen wannan shekara. Ƙasashen dake cikin tattaunawar sulhu sun haɗar da Amirka da Russia da Japan da Ƙasar Sin, a hannu ɗaya kuma da Koriya ta Kudu da kuma ta Arewa.