Ƙungiyar EU na shirin sake mayar da hulɗa da Zimbabuwe
July 24, 2012A ƙarshen taron da suka kammala a Brussels ministocin harkokin waje na ƙasahen ƙungiyar ta Tarrayar Turai sun ce zasu cire dukanin takunkumi da aka sakawa ƙasar , tare kuma da sake dawo da hulda da ƙasar wacce ƙungiyar ta dakatar a shekara ta 2002 bayan da aka gudanar da zaɓɓuɓuka cikin tashin hankali.
Ko da shi ke da farko wakilan ƙungiyar sun ce zasu ɗage takunkumi haramta zirga zirga da na hanna taɓa kuɗaɗen ajiya ga wasu jama'ar ƙasar guda 112,amma ban da wasu shika shikan da suka haɗa da shugaba Robert Mugabe, daga bisannin ƙungiyar ta sanar da cewa za ta iya cire har nasu inda komai ya tafi daidai,Aldo Dell Ariccio shi ne baban jami'in diflomasiya na ƙungiyar Tarrayar Turai a Hararre babban birnin zibabuwe''ya ce ƙungiyar ta tabbbatar da cewar shirya sahihin zaɓe na raba gardama cikin kwanciyar hankali, ba tursasawa ko yin barazana ga jama'a zai sa a cire sauran takunkumi ga jama'ar da suka yi saura.
Sharaɗin gudanar da sahihi zaɓe ga ƙasar ta Zimbabuwe, kafin cire takunkumi
Maganar amince wa da wani sabon kudin tsarin muli a ƙasar ta Zinbabuwe na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2008 tsakanin shugaba Mugabe mai shekaru 88 a duniya da kuma jagoran yan adawa morgan Tsvangirai wanda ke riƙe da matsayin framinsta akan wata gwamnatin haɗin kan ƙasa da ke zaman ganda garki ga afkawar ƙasar cikin yaƙin basasa.
Na ga ba ne ƙundin tsarin mulki da aka rubuta za a tabka muhawara akan sa a majalisar dokokin, sannan a yi Referudum akansa kafin a gudanar da zaɓɓuɓukan,To amma jam'iyyar Zanu PF ta Robert Mugabe ta bakin ɗaya daga cikin tsofin shika shikan ta, kana ministan shari'a Patrick Chinamasa ta mayar da martanni.''ya ce bamu son wata muhawara akan wannan batu ;amma abinda muke buƙata shi ne cire takunkumi ba tare dagiciya wasu sharuɗa ba.
Yan adawa na ƙasar ta Zimbabuwe na goyon bayan a cire takunkumi
Da alama dai ƙungiyar Tarrayar Turai da Amurka suka kaɗai suka dage kan matsayin na ci gaba da saka takunkumi inda;ƙungiyar Tarrayar Afikrka da ƙasahen Afirka ta kudu da Bostwana har ma da abokanan adawar Mugabe suna na buƙatar a ɗage takunkumi kamar yadda jagoran yan adwar Morgan Tchangarai ya baiyana a lokacin da ke yin ziyara a kasar Australiya. inda ya ce ya na da kyau a yi sasauci ga takunkumi saboda ƙara ƙwarin gwiwa ga waɗanda suka ƙaddamar da sauye sauye.''ya ce na san cewa a wani lokaci mun shiga wani yanayi na rashin tabbas a sa'ilin da aka riƙa samun asara rayukan jamaa, ya ce amma lokaci yayi ,na buƙatar samun hoɓasa na samun ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka ;ba kwai ba ya kasance ba Afrika ta zama yanki yuwan da cututuka da kuma yaƙe yaƙe, ya ce to Zimbabuwe ma na akan wanna turba´´
Ana sa ran za a gudanar da zaɓen a cikin watan okotoba, mai zuwa wataki ƙila akan ƙuria'ar ta raba gardama gabannin gudanar da sabin zaɓɓuɓuka a ƙasar ta Zinbabuwe.
Daga ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh