1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

020810 Referendum Kenia

August 3, 2010

A ran Laraba ne idan Allah Ya kai mu al'umar ƙasar Kenya za su kaɗa ƙuri'ar raba gardama akan sabon daftarin tsarin mulkin ƙasar

https://p.dw.com/p/ObAL
Mazauna sansanin tagayyararu a ƙasar KenyaHoto: DW

A dai halin da ake ciki yanzun ga alamu ba dukkan al'umar ƙasar ta Kenya da suka cancanta ne zasu samu kafar kaɗa ƙuri'a ba. Domin kuwa akwai dubban-dubatar waɗanda aka fatattaka daga yankunansu na asali sakamakon tashin-tashinar da ta ɓarke bayan zaɓen shugaban ƙasar ta Kenya daga aka gudanar misalin shekaru uku da suka wuce. Rahotanni masu nasaba da Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce har yau akwai kimanin mutane dubu arba'in dake zaune a sansanonin da aka tanadar musu, suke kuma cikin fushi game da gwamnati saboda haka ba zasu shiga ƙuri'ar raba gardamar ba.

Tashin-tashinar dai ta ɓarke ne bayan da aka ba sa sanarwar cewar shugaba Mwai Kibaki ɗan ƙabilar Kikuyu dake kan karagar mulki shi ne ya lashe zaɓen na watan disemban shekara ta 2007. Kai tsaye bayan haka faɗa ya ɓarke tsakanin Kikuyu da sauran ƙabilun ƙasar ta Kenya lamarin da ya haddasa asarar wuraren zaman sama da mutane dubu 60. Joseph Mburu, shi mai dai ɗan ƙabilar Kikuyu, da iyalinsa na daga cikin waɗanda wannan ƙaddara ta rutsa da su. Ya tsere tare da iyalinsa daga ƙauyensu ne bayan da 'yan ƙabilar Kalenjin suka afka musu suka kuma kashe mutane bakwai. Duka-duka abin da ya kuɓuta da shi shi ne rigar dake jikinsa, inda mayaƙan suka ƙone gidansu baki ɗaya. Ya ce tun daga wancan lokaci gwamnati tayi wa dubbannin mutanen da suka tagayyara alƙawarin taimako don sake farfaɗo da al'amuran rayuwarsu:

"A dai halin da muke ciki yanzu mun fida ƙauna a game da ikon sake komawa yankunanmu na asali. Duk da cewar rayuwarmu a can ta fi nagarta, amma tilas mu ci gaba da zama a nan duk da gurɓatacciyar rayuwar da muke ciki. Domin kuwa hakan shi ne mafi alheri a garemu akan komawa gun maƙiyyanmu. Muna iya komawa, amma kuma bayan shekaru biyar ko goma su sake ɓannatar da dukkan abin da muka gina. A sakamakon haka muka dace akan ci gaba da zama a nan."

Kawo yanzun dai ba abin da gwamnati ta taɓuka domin kyautata makomar rayuwar waɗannan tagayyararru. Daga baya-bayan nan ta gabatar da kuɗi kwatankwacin Euro miliyan biyar, amma ga alamu sun salwanta a hannun 'yan siyasa. Babbab abin da ya fi damun 'yan siyasar a yanzun shi ne ƙuri'ar raba gardama akan sabon daftarin tsarin mulkin ƙasar Kenya. Suna yawon yaƙin neman zaɓe a duk faɗin ƙasar, amma ba wani jami'in siyasar da ya leƙa sansanin Vumilia inda aka tsugunar da tagayyararrun. Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar Joseph Mburu ya ce faufau ba zai shiga ƙuri'ar raba gardamar ba:

"Ba zan shiga zaɓe ba. Saboda ban ga dalilin yin hakan ba, domin kuwa shi kansa ainihin zaɓen ne ma musabbabin fatattakarmu daga yankunanmu na asali. Wannan ƙuri'ar ta raba gardama zata haifar da wasu sabbin matsalolin. Idan har na samu taimako bayan ƙuri'ar raba gardamar to zan shiga zaɓe nan gaba. Amma wannan ƙuri'ar ba zata tsinana mini kome ba kuma ba na sha'awar shiga wasu sabbin matsaloli."

Da yawa daga mazauna sansanin na Vumilia na tattare da irin wannan ra'ayi. Ko da yake wata da ake kira Phylis Iwangui ta ce zata shiga zaɓen:

"Zan shiga zaɓen zan kuma ba da goyan baya ga sabon daftarin tsarin mulkin, saboda fatan da nike yi cewar hakan zata haifar mana da alheri nan gaba. Na karanta sabon daftarin duk kuma da cewar bai cika ɗari-bisa-ɗari ba, amma ya ƙunshi wasu manufofi masu nagarta, musamman ma dangane da maganar filaye."

Sabon daftarin dai ya tanadi bai wa dukkan mata da maza cikakken haƙƙin gadon filayen iyayensu, wanda kawo yanzu al'adun gargajiya na da yawa daga ƙabilun ƙasar Kenya ke haramta hakan.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal