Fatan 'yan Afirka a kan Donald Trump
November 7, 2024Donald Trumpya kafa tarihin sake farfadowa a siyasance, shekaru hudu bayan shan kayin da ya yi lokacin da ya nemi tazarce, bayan da Amurkawan suka ki sake zabarsa, sakamakon irin katobarar da ya rinka tabkawa a mulkinsa, wanda yanzu haka jiran hukunci yake kan tarin tuhume-tuhumen da ke gaban kotu a kansa, ciki har da batun tunzura magoya bayansa har suka tayar da tarzomar far wa cibiyar gudanar da mulkin kasar, a yunkurinsu na haifar da tarnaki ga shirin mikawa sabon shugaba Joe Biden mulki a lokacin. Firaministan Habasha Abiy Ahmed na daga cikin shugabannin Afirka da suka mika sakon taya murna ga Mr Trump, kamar yadda ya wallafa shafinsa na X, yana mai fatan aiki da shi don karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
Haka batunyake daga bangaren shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, wanda ya ce kasarsa a shirye take ta hada karfi da karfe da Amurka karkashin Trump, don sake gina duniya mai cike da zaman lafiya. Shi kuwa a na sa bangaren shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar, ya ce da hadin gwiwar Shugaba Trump, za su iya yaukaka dangantakar bunkasa tattalin arziki da karfafa zaman lafiya, har ma magance kalubalen da kasashen biyu ke fuskanta. Freeman Bhengu shi ne jagoran jam'iyyar Sofasonke a Afirka ta Kudu, ya bayyana wa DW farin cikinsa kan samun nasarar Donald Trump, kasancewar ra'ayinsu ya zo daya a fagen siyasa.
'' Mun ji dadi matuka da wannan nasara, kasancewar muna da akida iri daya da shi a kan batun rufe iyakokin kasa, domin dakile kwararar bakin haure masu shiga ta barauniyar hanya. Hakan zai kara mana azama a Afirka ta Kudu wajen yaki da masu shigowa kasar ba bisa ka'ida ba''. Fahimta aka ce fuska, domin wani mazaunin birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu Eric Matthews na da sabanin ra'ayi da Mr Bhengu.
''7Ina jin wasu abubuwa na dabam, a gefe guda kuma ina fatan Trump din zai taimaka wajen farfado da Afirka ta Kudu daga halin da ta ke ciki yanzu haka, musamman batun farashin dalar Amurka da kudinmu wato Rand. Hakika muna cikin mawuyacin hali, ba zan boye ba, talauci ya kwantar da mu. Idan har ya yi mana wannan kokari to lallai za mu ji dadi kuma za mu taya shi murna''.Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da alaka mai kyau da Amurka kamar yadda take don ciyar dakasarsa gaba.