1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Baghdadi ya fitar da sakon murya

Abdul-raheem Hassan
September 29, 2017

Kungiyar IS ta fitar da wani faifain sautin muryar da take ikirarin na shugaban ta ne Abu Bakr al-Baghdadi, a sakon muryar an jiyo shi yana karfafa gwiwar 'yan kungiyar da ke fafatawa a kasashen Iraki da Siriya.

https://p.dw.com/p/2kwLZ
Abu Bakr al-Baghdadi Führer Islamischer Staat
Shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-BaghdadiHoto: Getty Images/AFP

A cikin sakon da aka nada al-Baghadadi ya kirayi magoya bayansa, ka da su sassauta kai hare-hare ga gidajen yada labaran kasashen duniya da suke sukar kungiyar. To sai dai kawo yanzu babu tabbacin lokaci da kuma inda aka nadi sautin muryar da kafar yada labaran Al-Furqan ta wallafa.

Wannan dai shi ne karon farko da aka ji duriyar shugaban kungiyar al-Baghdadi kusan shekara guda, tun bayan da kasar Rasha ta yi ikirarin halaka shugaban a farkon shekarar 2017, ikirarin da ya haifar da cece-ku-ce tsakanin Rasha da Amirka. To sai dai kasar Amirka ta ce ta babu dalilin yan ta baba a kan wannan sabon faifai na murayar shugaban kungiyar IS din da aka wallafa, amma dai ta ce ta na ci gaba zurafafa bincike.

A baya dai an sanya tukuicin kudi da ya kai dalar Amirka miliyan 25, ga duk wanda ya yi nasarar kashe shugaban kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi amma har yanzu babu wanda ya fito ya ba da tabbacin labarin inda shugaban yake.