Al Shabaab ta kashe sojojin Somaliya 61
June 8, 2017Talla
Sabbin bayanan da ke fitiwo daga yankin, sun ce sama da mutane 60 ne suka mutu a artabu tsakanin sojojin gwamnati da mayakan na Al Shabaab. Mayakan na Al Shabaab sun kuma yi awon gaba da wasu motocin sintiri na sojojin ta re da kone wasu kurmus.
Galibin wadanda suka mutu dai jami'an sojin ne kamar yadda Al Shabaab din ta yi ikirari. Sai dai kamar yadda gwamnan yankin Bari, Yusuf Mohamed ya tabbatarwa kamfanin labaran Reuters, ba a kai ga tabbatar da yawan wadanda suka mutu ba, sai dai ya shaidar da kasancewar sojoji a sansanin da ya fuskanci harin.