Al'ummar Kenya na zaman makoki
September 26, 2013Talla
Daga ƙarshen makon da ya gabata ne al'ummar Kenya ta shiga cikin wani yanayi na juyayi bayan da suka wayi gari mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon harin wasu 'yan ta'adda a wata cibiyar cinikiyya da ke babban birnin ƙasar.
Jami'an tsaron ƙasar tare da tallafin wasu ƙwararru sun shafe kwanaki huɗu suna musayar wuta da 'yan ta'addan kafin su samu suka ci ƙarfinsu. Sai dai iyalai da dama sun yi asarar 'yan uwa da abokan arziƙi a dalilin wannan hari. A ƙasa mun yi muku tanadin rahotannin da muka hada a wannan lokacin