Taro kan rikicin Siriya
May 9, 2013Mutane da dubu 70 ne dai suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu a yakin basasan kasar Siriya da ya biyo bayan boren hambarar da shugaba Bashar al Assad. A dai halin yanzu ana ci gaba da nuna fargabar cewa mai yiwuwa ne yakin ya yadu zuwa sauran yankin Gabas ta Tsakiya, kasancewar duk yunkurin da aka yi na kawo karshen fadan ya ci tura. A kan haka ne kasashen Rasha da Amirka ke neman yin hadin gwiwa wajen shirya taron kasa da kasa don lalubo mafita daga rikicin kasar ta Siriya
Baki ya zo daya tsakanin Rasha da Amirka
Yayin ganawarsa da takwaransa na Rasha, Sargei Lavrov a birnin Moscow sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry ya ce za a gayyaci wakilan gwamnatin Assad da na 'yan adawa zuwa taron da zai gudana a watan Mayu. Lavrov shi kuma cewa ya yi yanzu an gano muhimmacin ba da kwarin gwiwar samun mafita ta siyasa daga rikicin na Siriya. Volker Perthes, shugaban gidauniyar kimiyya da siyasa da ke birnin Berlin ya yaba da hakan a matsayin gagarumin mataki.
"Wannan wani mataki ne mai kyau. Ya dace Amirka da Rasha su yi aiki tare don samun mafita daga wannan rikici. Saboda da tsoron cewa Siriya za ta kara kambama gwagwarwayar kwace iko da ake yi a wannan yanki tsakanin Katar da saudiya da Iran da kuma sauran kasashe ba."
Ita dai zanga-zangar limana da 'yan kasar suka shiga da farko don aiwatar da sauye-sauyen siyasa yanzu ta rikida zuwa yakin da yan Shi'a da Sunni ke da wakilici a cikinsa inda a lokacin da a hannun daya Iran ke goyon bayan gwamnatin Assad Katar da Saudiya a dayan hannun ke goyon bayan 'yan adawa.
Yayin ganawarsa da takwaransa na Amirka, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce damuwarsu ba ita ce abin da ka iya cikawa da wani bangare na al'umar siyara ba, damuwarsu ita ce makomar baki dayan al'umar kasar ta Siriya. Su dai kasahen Rasha da China har sau uku suka hau kujerar na ki game da kudurin daukar mataki akan rikicin na Siriya da ya hada da yin matsin lamba ga shugaba Bashar al-Assad. A maimakon haka Rasha ta gabatar da wani kuduri na gaban kanta a bara, to amma sa aka yi fatali da shi. Akan hakan ne Volker Perthes ke dasa ayoyin tambaya game da karfin fada a ji da Rasha ke da shi akan Siriya da kuma yadda za ta kaya gun wannan taro.
Tsoron yiwuwar samun gibi na iko a Siriya
Amirka da Rasha dai sun gano bukatar shirya taron ne bayan da Isra'ila ta kai hare-hare kan wasu wurare da ke kusa da birnin Damasakus a 'yan kwanaki da suka gabata. Ita kuma Siriya ta yi barazanar yin ramuwar gayya- abin da ake ganin zai tsunduma Amirka a cikin rikicin a matsayinta na kawar Isra'ila-matakin da shi kuma shugaba Barack Obama bai muradin dauka. Damuwar da ake nunawa akan sabon shirin na Siriya dai ita ce mai yiwuwa ne a samu gibi na iko da zaran an wargaza gwamnatin Assad. Abin da Guenther Meyer, shugaban cibiyar nazari akan kasashen Larabawa da ke jami'ar Mainz a Jamus ke ganin shi ne dalilin da ya sa Barack Obama ke neman samun mafita ta siyasa-gibin da kuma a cewarsa kungiyoyin masu alaka da Alka'ida irin su al-Nusra za su cike, yana kuma ma kashedi game da kasancewar Siriya markafafa irinta mafi karfi ga Alka'idar. Meyer ya kara da cewa:
"Ina gani za a fuskanci matsaloli. Da farko akwai batun tsagaita wuta. Wata matsalar kuma ita ce rarrabuwar kawuwa da ake samu tsakanin 'yan tawayen. Wannan matsala ce da babu makawa za a fuskanta ko da ma 'yan tawayen "Free Syria Army" da sauran kungiyoyi sun amince da shirin tsagaita wuta."
Taron da za a shirya akan Siriya zai gudana ne daidai da matsayin da aka cimma a birnin Geneva a ranar 30 ga watan Yuni shekarar 2012 inda kasashe masu ikon hawa kujerar na ki a Majalisar Dinkin Duniya da Turkiya da sauran kasashen Larabawa suka daidata kan shirin samar da mafita ta siyasa daga rikicin kasar ta Siriya.
Mawallafiya: Diana Hodali/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu
Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.