Amirka na neman karfafa karfin sojin Ukraine
April 26, 2022Sakataren tsaron Amirka ya ce kasarsa ta kuduri aniyar matsa kaimi don ganin Ukraine ta samu nasara a kan Rasha da ta mamaye ta. Lloyd Austin ya yi wannan furunci ne a yayin bude taron da Jamus ke daukar bakunci don karfafa karfin soji na fadar mulki ta kyiv.
Kimanin wakilan kasashe 40 ne suka hallara a sansanin sojin saman Amirka da ke Ramstein a yammacin Jamus, a daidai lokacin da Berlin ta sanar cewa za ta ba da izinin mika wa ukraine motocin sulke. Wannan matakin dai na zama wani babban sauyi a manufofin taka-tsantsan da Jamus ke bi wajen tallafa wa Ukraine.
Ita dai Amirka da ke ba da mafi yawan taimakon soji ga Ukraine, tana son ba ta nau'in makaman atilare da harsasai da za su yi tasiri a wannan yaki da Rasha, a cewar ma'aikatar tsaro ta Pentagon. Dama Ukarine na ci gaba da neman taimakon manyan bindigogi da makamai a kokarin da take na fatattakar sojojin kasar Rasha a kudanci da gabashin kasar.