Amirka ta cilla makami mai linzami
May 31, 2017Talla
Mahukuntan na Amirkar dai sun ce makamin mai linzami yana da karfi ne na tafiya daga nahiya zuwa wata nahiya.
Tuni kuwa suka bayyana harba makamin da cewar mataki ne na kanda-garki ga barazanr da Amirkar ke fuskanta daga zabure-zaburen kasar koriya ta arewa.
Tun a bara ne dai kasar Koriya ta arewa ta daage da harben-harben makamai masu linzamin da ta ce na kare kanta ne daga barazana musamman daga Amirka.
Kasar Amirka dai tana da sabbin makaman da ke iya cin tazarar kilomita dubu 10, yayin da tazararta da Koriya ta arewa ke kilomita dubu 9.