1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya dakatar da tattaunawa da Taliban

September 8, 2019

Shugaba Donald Trump na kasar Amirka, ya sanar da dakatar da tattaunawar sulhu tsakanin wakilan gwamnatin Amirka da kuma 'yan kungiyar mayakan Taliban.

https://p.dw.com/p/3PEVy
Donald Trump
Hoto: picture alliance/dpa

Shugaban na Amirka wanda ya sanar da hakan a wani sakon twitter da ya wallafa a daren ranar Asabar, ya ce ya dakatar da tattaunawar ce bayan wani hari da kungiyar Taliban din ta kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 ciki har da wani sojin Amirka.

Kungiyar Taliban ta tabbatar da kisan mutanen a harin da ta kaddamar a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, a ranar Alhamis. 

Shugaba Trump yace ya yi mamakin yadda kungiyar da ake kokarin sasantawa da ita, ke kashe mutane a matsayin nuna karfin samun rinjaye a tattaunawar, yana mai cewa kamata ya yi su dakatar da kai hare-hare.

Wani zama na tara a jerin wadanda aka yi tsakanin wakilan Amirka da na Taliban a birnin Doha na kasar Katar, ya dai kyautata fatan yiwuwar samun zaman lafiya a Afghanistan, kasar da ke fama da yaki tsawon shekaru 18.