Amurka da Burtaniyya sun kai hari kan 'yan tawayen Houthi
January 23, 2024Sojojin Amurka da na Burtaniyya sun kai wani sabon harin bama-bamai a kasar Yemen a daren Litinin zuwa Talata kan 'yan tawayen Houthi, wadanda ke ci gaba da kai hare-hare a tekun Baharmaliya, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a Gaza. Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, Washington da London sun yi nuni da cewa, sun kai harin ne bisa goyon bayan Canada da Bahrain da Holland, kan wasu wurare takwas masu muhimmanci ga 'yan Houthi.
Karin bayani:Amurka ta kai sabbin hare-hare kan Houthi a Yemen
Kasashen biyu sun ce burinsu shi ne dawo da kwanciyar hankali a kewayen Tekun Bahar Maliya, inda suka yi gargadin cewar ba za su yi jinkirin kare rayuka da zirga-zirgar cinikayya cikin 'yanci a magudanar ruwa masu muhimmanci a duniya ba. A cewar kamfanin dillancin labarai na Houthi, Saba, sojojin Amurka da Burtaniya sun kai hari kan babban birnin Sanaa da wasu lardunan kasar da kuma sansanin sojin da ke arewacin Sanaa.
Karin bayani:Houthi ta harba makami mai linzami kan jirgin ruwa
'Yan tawayen Houthi ne ke rike da yanki mai yawa na kasar Yemen, bayan shafe kusan shekaru 10 suna yaki da dakarun gwamnati da ke da goyon bayan Saudi Arebiya. Amma kuma kasar da ke zama mafi talauci a yankin Larabawa, tana cikin wani yanki mai muhimmanci na zirga-zirgar jirage da kuma kasuwanci a teku.