Houthi ta harba makami mai linzami kan jirgin ruwan Girka
January 16, 2024A cewar wani kamfanin da ke kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin ya ce harin ya lalata wani bangare na jirgin da ke kan hanyar zuwa Isra'ila ta mashigin Suez, duk da cewar rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin dakon kayan na Girka na ci gaba da nausawa zuwa Isra'ailan.
Ko a baya bayannan, sojin ruwan Amurka sun kakkabo wasu makamai masu linzami na mayakan Houthi da suka harba kan wani jirgin ruwan Amurka, duk da cewa mayakan na Houthi sun yi nasarar harba wani makami mai linzami kan wani jirgin ruwan Amurka a gabar tekun Oman.
Hukumar da ke tattara bayanan shige da ficen jiragen ruwan karkashin kulawar Burtaniya ta akwai rahoton kai hari yankin gabar arewa maso yammacin Saleef a Yeman, duk da ba su bayar da cikakken rahoton kai harin ba.
.