1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta aike da jirgin ruwa dauke da kayan agaji zuwa Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 10, 2024

Tun a shekarar 2007 ne Isra'ila a datse gabar ruwan shiga Gaza, bayan da kungiyar Hamas ta kwace ikon Zirin

https://p.dw.com/p/4dM5L
Hoto: Marcos Andronicou/AP/dpa/picture alliance

Rundunar sojin Amurka ta aike da jirgin dakon kaya na ruwa dauke da kayan agaji zuwa Gaza, kwanaki kadan bayan da shugaba Joe Biden ya alkawarta gina gadar ruwa ta wucin-gadi don shigar da agaji Gaza, kamar yadda cibiyar kula da harkokin tsaron Amurka CENTCOM ta tabbatar a Lahadin nan.

Karin bayani:Chaina ta nemi Isra'ila ta daina kashe fararen hula a Gaza

Jirgin na dauke da tarin kayan agaji da kuma kayayyakin da za a yi amfani da su na tabbatar da samar da tashar ruwan, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa annobar yunwa ta galabaitar da al'ummar Gaza.

Tun a shekarar 2007 ne Isra'ila a datse gabar ruwan shiga Gaza, bayan da kungiyar Hamas ta kwace ikon Zirin.

Tuni dai aka jiyo hukumar leken asirin Isra'ila MOSSAD na cewa tattaunawa ta yi nisa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yakin Gaza, yayin da ake dab da fara azumin watan Ramadan.

Karin bayani:Za a koma kan tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza

Shugaban hukumar David Barnea ne ya tabbatar da hakan, bayan ganawa da takwaransa na CIA ta Amurka William Burns, kamar yadda MOSSAD din ta sanar.

Kasashen Masar da Qatar da kuma Amurka ne ke jagorantar tataunawar sulhun, don kawo karshen yakin da aka shafe sama da watanni biyar ana gwabzawa.