Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya
April 12, 2024Wani jami'i a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagone da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce Amurka ta dauki wannan mataki da nufin dakile duk wata barazana ta Iran da kuma kare muradunta a yankin.
Karin bayani: Kasar Iran ta sha alwashin mayar da martani
Sai dai a daidai lokacin da Washington ta sanar da wannan mataki, ministan harkokin wajen Italiya ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Iran da nufin yayyafa ruwan sanhi ga wannan sabon rikici da ke shirin daukar dumi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Karin bayani: Amurka da Burtaniya sun kai sabbin hare-hare Yemen
A cikin wata sanarwa da ya fidda jami'in diflomasiyyan na Italiya Antonio Tajani ya ce ya rarrashi hukumomin fadar Taheran da ta kai zuciya nesa.
Kazalika ya kuma bukaci Iran da ta kwantar da hankulan kungiyoyi masu alaka da ita a yankin da su guji tayar da fitina don kauce wa barkewar gagarumin rikici da ba a san karshensa ba.