Amurka da Burtaniya sun sake kai hari Yemen
February 4, 2024A cikin wata sanarwar hadin gwiwa Amurka da Burtaniya sun ce sun kai wadannan hare-hare a ranar Asabar 03.02.2024 a kan mabuyar 'yan tawayen Houthi 36 a wurare 13 da ke kasar Yemen la'akari da ci gaba da tarnakin da 'yan tawayen ke kawo wa zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa da na kasuwanci da kuma jiragen ruwan yaki masu ratsawa ta Tekun Bahar Maliya.
Karin bayani: Amurka da Burtaniyya sun kai harin bama-bamai kasar Yemen kan 'yan tawayen Houthi
Jim kadan bayan sabbin hare-haren kakakin 'yan tawayen na Houthi Nasr al-Din Amer ya wallafa cewa muddin ba a samar da zaman lafiya a Gaza ba, ba za su bari kwanciyar hankali ta yalwata a yankin ba.
Karin bayani:
Samamen hadin gwiwar da ke zama karo na uku da kasashen kawaye ke kai wa 'yan Houthi na zuwa ne washegarin hare-haren daukar fansa da Amurka ta kai a Iraki da Siriya kan mutuwar sojojinta uku a kudancin kasar Jordan a ranar 28 ga watan Janairu.