1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka za ta ba wa Ukraine tallafin makamai

Abdoulaye Mamane Amadou
October 16, 2024

A daidai lokacin da wasu kasashe aminan Ukraine ke fatan sulhunta rikicin da kasar ke yi da Rasha, gwamnatin Amurka ta kara wa kasar sabon kunshin tallafin makamai don kare kanta.

https://p.dw.com/p/4lsxW
Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da Volodymyr Zelensky ta wayar tarho
Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da Volodymyr Zelensky ta wayar tarhoHoto: White House/ZUMA Press Wire Service/picture alliance

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da wani karin kunshin tallafin makamai na dala miliyan 425 ga Ukraine, wanda yake zuwa a daidai lokacin da kawayen Ukraine ke neman ko ta halin kaka su warware zaren rikicin da ya sarke a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna.

Fadar White House ta ce a yayin tattaunawar da shugaba Biden ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ne ya tabbatar da masa da sabon kunshin taimakon, wanda zai ta'allaka musamman ga makaman kare sararin samaniya da tankokin yaki.