An fara fatattakar IS a Tal Afar na Iraki
August 20, 2017Talla
Firaministan Iraki Haider al-Abadi ya sanar da fara kaddamar da hare-haren neman kwato Tal Afar, wani muhimmin yanki na arewacin kasar da ke hannun mayakan IS. Tal Afar dai ita ce tunga ta karshe da kungiyar ta IS ke rike da ita a shiyar. Sanarwar da ta fito da safiyar wannan Lahadi, na zuwa ne kimanin wata guda da kwace birnin Mosul daga ikon mayakan na tarzoma, wani abin da ke matsayin babban nakasu ga kungiyar.
A cewar Firaministan na Iraki, jami'an tsaron Hashed al-Shaabi da 'yan sanda da jami'an murkushe tarzoma, baki dayansu ne za su taimaka wa dakarun sojin kasar a yakin. Da ma dai dakarun na tsananta kai hare-haren neman kwato wasu muhimman biranen Irakin da kungiyar IS ke iko da su.