1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramta wa Imran Khan rike mukami a Pakistan

October 21, 2022

Hukumomi a Pakistan, sun dauki matakin hana tsohon firaministan kasar damar aikin da ya shafi jama'a saboda zargin taka dokoki da ya yi a zamanin da yake rike da gwamnati.

https://p.dw.com/p/4IWYI
Pakistan Imran Khan
Hoto: Aamir Qureshi/AFP

Hukumar zabe a Pakistan, ta haramta wa tsohon firaministan kasar Imran Khan damar rike duk wani mukami na gwamnati na tsawon shekaru biyar.

Hukumar zaben ta zargi tsohon firaministan na Pakistan ne da laifin sayar da wasu kyautuka da aka bai wa gwamnatin lokacin da yake mulki, da ma wani laifin na boye wasu kadarorin.

Jami'ai da sauran masana shari'a a kasar ta Pakistan, sun ce abin da hukumar zaben ta yi na iya sanya Imran Khan ya rasa kujerarsa ta majalisar dokoki.

Sai dai ana kallon wannan mataki na hukumar zaben kan Imran Khan, na iya dagula al'amuran siyasar Pakistan mai fama da tarin matsalolin musamman na rashin ci gaba.