An kaddamar da gagarumin bincike kan shugaban Koriya ta Kudu
December 5, 2024Masu shari'a a Koriya ta Kudu sun kaddamar da wani bincike kan shugaban kasar Yoon Suk Yeol da ministan harkokin cikin gida da kuma tsohon ministan tsaro bisa hannu a yunkurin kafa dokar soji a kasar.
Kim Yong-hyun wanda ya yi murabus daga mukaminsa na ministan tsaro biyo bayan hannu a kokarin kafa dokar ta soji a ranar Talata zai kuma fuskanci takunkumi kan tafiye-tafiye a yayin da ake gudanar da biciken.
Koriya ta Kudu: 'yan siyasa da kungiyoyin kwadago sun bukaci shugaban kasa ya yi murabus
Shugaban na Koriya ta Kudu ya kafa dokar ce bayan zargin barazana daga wasu jami'an soji da 'yan adawar siyasa da bai bayyana su ba.
Sai dai bayan sa'o'i shida, Yoon ya janye dokar bayan da majalisar dokokin kasar ta nuna adawa da ita bayan kada kuri'a.
Shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol na fuskantar matsin lamaba daga bangaren adawa da kuma jam'iyyarsa ta PPP da ta nemi ya yi murabus ko kuma ta tsige shi sa'o'i kadan bayan da ya ayyana dokar soja wacce daga bisani bore ya tilasta masa janyewa.
Koriya ta Kudu ta bayyana damuwa kan alakar Rasha ta Koriya ta Arewa
A yanzu za a kada kuri'a kan ko za a tsige shugaban kasar ko kuma a'a a ranar Asabar mai zuwa.