Koriya ta Kudu: An bukaci Shugaba Yoon ya yi murabus
December 4, 2024Shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol na fuskantar matsin lamaba daga bangaren adawa da kuma jam'iyyarsa ta PPP da ta nemi ya yi murabus ko kuma ta tsige shi sa'o'i kadan bayan da ya ayyana dokar soja wacce daga bisani bore ya tilasta masa janyewa.
Karin bayani: An shiga rudani bayan shugaban Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci
A cikin wata sanarwa da aka yada a kafar talabijin a wannan Laraba jam'iyyar shugaban ya jaddada cewa dole Yoon Suk Yeol ya girbi abin da ya shuka kan wannan hali da yi yi yunkurin jefa kasar a ciki. Kazalika da sanhin safiyar Laraba babban jami'in fadar shugaban kasar da wasu dumbin mukarrabansa sun mika takardar murabus kamar yadda kamfani dillacin labarai na Yonhap ya ruwaito.
A daya gefe kungiyar kwadago ta Koriya ta Kudu mai membobi sama da miliyan 1,2 ta kira yajin aikin gama gari har sai Shugaba Yoon ya yi murabus.
Tuni kasashe kawayen Koriyar ciki har da Amurka da Burtaniya da kuma Japan suka fara nuna damuwa kan wannan rikicin siyasa da ya kunno kai yayin da Chaina ta bukaci 'yan kasarta da ke Koriyar da su zauna a guri maras hadari.