An kafa dokar hana fita a fadin Faransa
March 17, 2020Harkoki sun tsaya cik a fadin kasar Faransa, kasa ta baya-bayan nan da hukumomi suka tsaurara matakan hana zirga-zirgar miliyoyin jama'a sakamakon
'Yan sanda dubu 100 ne aka baza, wadanda za su tabbatar da wannan dokar, wadda za ta kai kwanaki 15 tana ci a fadin kasar.
Shugaba Emmanuel Macron, ya bayyana halin da ake ciki dangane da cutar tamkar na yaki.
Sojoji a cewar Shugaba Macron za su tallafa wa asibitoci da ke fama da tarin ayyuka na gaggawa.
Gwamnatin Faransar ta kuma ware euro biliyan 300, da za ta yi amfani da su wajen tallafa wa masa'antun da ma'aikatan da suka shiga garari ta dalilin wannan annoba.
Za kuma a ci duk wani da ya yi bijire wa dokar tarar da ta kama daga euro 38 zuwa 135.
Mutum 146 ne dai suka mutu da cutar a Faransar, sama da 6,600 kuwa ke dauke da ita ya zuwa yanzu.