An kai hari a rumfar zabe a Pakistan
July 25, 2018An kaddamar da hari a wajen da jama'a ke kada kuri'a zabe a babban zabe da ake gudanarwa a kasar Pakistan a wannan Laraba, inda dubban jama'a ke taruruwa don sauki nauyinsu na 'yan kasa.
Kimanin mutum 30 ne suka mutu sama da wasu 40 kuma suka jikkata a harin da aka kai a yankin kudu maso yammacin kasar.
Da fari dai hukumomi sun baza jami'an tsaro masu yawa a galibin rumfunan, bayan barazanar da kungiyar 'yan ta'adda ta yi na kai hare-hare da nufin hana zaben.
An dai fara zabe ne da karfe takwas na safiya, za kuma a kulle karfe shida ne na yammaci a dukkanin sassan kasar.
Sama da 'yan kasar ta Pakistan miliyan 100 ne aka yi wa rajista, akwai kuma 'yan takaran majalisar kasa sama da dubu 11.
Kungiyoyin IS da Taliban dai sun ce za su tarwatsa zaben da boma-bomai, saboda adawar da suke yi da tsarin jagoranci na dimukuradiyya da suka kafirta.