An kai hari kan dalibai a Japan
May 28, 2019Talla
Hukumomi a Japan, sun tababatar mutuwar akalla mutum uku yayin da wasu 16 da suka hada da yara 'yan makarantar fimarare suka ji rauni a harin.
Lamarin da ya faru a yankin Kawasaki kusa da birnin Tokyo, ya rutsa ne da 'yan matan da tsakanin shekaru shida zuwa bakwai ba, a lokacin da suke jiran motar bas da za ta kai su wata makaranta.
Akwai ma daya daga cikin 'yan matan da ta rasa ranta a cewar rahotanni a safiyar Talata.
'Yan sanda sun ce wani mutum da suke tsare da shi ma, ya mutu sakamakon daba wa kansa wuka da ya yi a wuya.
Hukumomi sun ce ba kai ga tabbatar da dalilin maharin na aikata wannan aikin ba, sai dai an ji shi yana ihun cewa ''sai na kashe ku''.
Japan dai na daga cikin kasashen da ke manan lafiya a duniya.