1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kama mayanan Taliban a Afghanistan

July 25, 2021

Dakarun kasar Afghanistan sun kama wasu mayakan Taliban hudu ciki har da wani kwamandansu da ake zargin su da hannu harin rokoki da aka kai fadar shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3y1W4
USA I Washington I Afghanistans Präsident Ashraf Ghani und Präsident Joe Biden
Hoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Dakarun kasar Afghanistan sun kama wasu mayakan Taliban hudu ciki har da wani kwamandansu da ake zargin su da hannu cikin harbe-harbe rokoki da aka kai kan fadar shugaban kasa.

Akalla rokoki uku ne dai aka harba zuwa fadar Shugaba Ashraf Ghani a ranar Talata lokacin da ake tsaka da Sallar idi.

Ministan da ke kula da harkokin cikin gida, ya ce 'yan sandan Afghanistan ne suka kama mayakan na Taliban a wani sintiri a birnin Kabul jiya Asabar, kamar yadda ya tabbatar da labarin a yau Lahadi.

A bara ma dai an kai wa fadar shugaban kasar hari, lokacin da ake rantsar da Shugaba Ashraf Ghani karo biyu, harin da kungiyar IS ta dauki alhaki.

Mayakan na Taliban dai na samun galaba a Afgahnistan a yanzu, bayan janye sojojin Amirka da na kungiyar tsaro ta NATO da aka yi a baya-bayan nan.