An kashe 'yan IS a Masar
April 11, 2017Talla
Ministan cikin gidan kasar ta Masar, ya ce da farko dai yan bindigar IS din sun budawa 'yan sanda wuta su kuma 'yan sandan suka mayar da martani. An zargi mayakan na IS da kokarin kai harin ta'addanci kan wasu majami'u da gidajen mabiya addinin Kirista da wasu muhimman cibiyoyin tsaro da ma na tattalin arziki.
Wannan artabun na zuwa ne kwana guda da kaddamar da wasu hare-haren bama-bamai kan majami'u biyu a biranen kasar biyu, da suka snadiyyar mutuwar akalla mabiya 46. Kazalika akwai wasu sama da mutum 100 da suka jikkata a hare-haren ranar Lahadin da ta gabata.