Hawa teburin tataunawa a kan kogin Nilu
September 23, 2023Talla
Wannan na zuya ne bayan da Habasha ta sanar da kammala mataki na 4 kuma na karshe na cike kogin, matakin da ya janyo martani mai zafi daga Masar da suka kira lamarin da haramtacce. Wannan ne zama na biyu a tattaunawa tsakanin kasashen 3 da ke gudana a yau din nan a birnin Addis Ababa, inda Habasha ke cewar tana fatan su cimma matsaya cikin kwanciyar hankali.
Masar da Sudan na kukan sabon aiki a madatsar ruwan ka iya kaisu ga karancin ruwa. Sai dai ko kafin yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin nan da shekarar 2025 Masar ka iya shiga kangi na rashin ruwa da kuma wani sashi na kasar Sudan biyo bayan wannan mataki na cike madatsar ruwan Nilu.