An sako daliban garin Tegina a Najeriya
August 27, 2021A ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata ne dai 'yan bindiga dauke da muggan makamai suka kwashe dalibai 136 tare da malaminsu, daya daga cikin jerin sace-sacen daruruwan dalibai da masu garkuwa da mutane ke yi a Najeriya.
Shida daga cikin daliban dai sun rasa rayukansu a lokacin da suke hannun 'yan bindigar, yayin da 15 kuwa suka kubuto.
Jagoran makarantar Islamiyyar ta Salihu Tanko, Abubakar Alhassan, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da sakin daliban, sai dai bai ce komai game da biyan kudin fansa ba.
Wasu ruwayoyin da aka jiyo daga wasu jami'ai dai, sun ce an biya maharan kudade kafin su kai ga sakin daliban sama da 100.
Tun cikin watan Disambar bara ne dai lamarin satar dalibai da wasu manyan mutane ya kazanta a Najeriyar, inda 'yan bindigar ke kwashe mutanen suna karbar makudan miliyoyi na fansa.